Ƴan Sanda sun kama ƴan ta’addan da suka shigo Kano daga wasu jihohi

0
16

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta sanar da kama wasu mutane biyar da ake zargi da aikata garkuwa da mutane da kuma satar shanu, a wasu ayyukan sirri daban-daban da aka gudanar a kananan hukumomin Kiru da Tsanyawa.

Sanarwar ta fito ne daga bakin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda ya ce an samu nasarar kama mutanen ne a ranar 14 ga Disamba, 2025, biyo bayan umarnin da Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayar.

A cewar sa, jami’an sashin yaki da garkuwa da mutane na rundunar (Anti-Kidnapping Squad) sun kai samame a yankin Rahma Round da ke karamar hukumar Kiru, bayan samun sahihin bayanan sirri. 

A yayin wannan samame, jami’an sun kama mutane hudu da ake zargi, ciki har da wani mai suna Shafiu Ibrahim, mai shekaru 25, daga kauyen Auchanawa da ke karamar hukumar Ikara a Jihar Kaduna.

Binciken farko ya nuna cewa Shafiu Ibrahim ya amsa laifin kasancewa mamba a wata kungiyar masu garkuwa da mutane, tare da shiga wasu ayyukan satar shanu. 

Rundunar ta ce ta kwato babur kirar TVS daga hannun sa, yayin da ake ci gaba da bincike kan rawar da sauran mutum ukun da aka kama suka taka a wasu laifuka daban-daban.

A wani aikin hadin gwiwa kuma, jami’an sashin yaƙi da garkuwa da mutane  da ofishin ‘yan sanda na Tsanyawa sun kama wani matashi mai suna Bishir Umar, dan shekara 24, dan karamar hukumar Karaduwa a Jihar Katsina. 

An kama Bishir ne a kauyen Mahuta da ke karamar hukumar Tsanyawa.

Rahotanni sun nuna cewa wanda ake zargin ya amsa shigowa jihar Kano tare da wasu abokan aikin sa guda biyu a kan babura, dauke da bindiga, domin aikata munanan laifuka. 

An cafke shi ne yayin da yake leka wurare, yayin da sauran abokan nasa suka tsere da babura da bindiga.

Rundunar ‘yan sandan ta tabbatar da cewa za a gurfanar da dukkan wadanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike. 

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yabawa al’umma bisa hadin kai da suke bai wa jami’an tsaro, tare da kira gare su da su kasance masu sa ido da kuma gaggauta kai rahoton duk wani abu da ake zargi zuwa ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko ta lambobin gaggawa na rundunar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here