Yadda ƙirƙirarriyar basira (AI) ta taimaka wajen yaɗa labaran ƙarya a shekarar 2025

0
11

A shekarar 2025, da muke bankwana da ita kafafen sada zumunta a Najeriya sun cika da labaran ƙarya da bayanai marasa tushe, lamarin da ya ƙara tsananta sakamakon yawaitar amfani da ƙirƙirarriyar basira wato Artificial Intelligence (AI). 

A tsawon shekarar, mutane da dama sun tsinci kansu suna tambayar ko wani bidiyo ko hoto na gaskiya ne ko kuma na AI, ne abin da ke nuna irin yadda fasahar ta rikitar da sahihancin bayanai.

Binciken ya nuna cewa an yi amfani da hotuna, bidiyo da sauti na AI wajen ƙirƙirar labaran ƙarya musamman a fagen siyasa, tsaro, tattalin arziki da lafiya. 

Wasu masu amfani da kafar sada zumunta sun yi amfani da AI wajen ƙirƙirar bidiyo da hotunan shugabanni domin yaɗa zancen da ba na gaskiya ba ko ɓata suna.

Daga cikin manyan misalai akwai bidiyoyin ƙarya da aka danganta da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, inda aka nuna shi yana barazana ga ‘yan ƙasa kan batun AI. 

Haka kuma, an ƙirƙiri hotunan AI na Gwamnan Benue, Hyacinth Alia, ana nuna kamar ana gina gumakan sa a zagayen hanyoyi, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce.

A wani bangare, an yi amfani da hotunan AI da bidiyo wajen tallata damfarar hanyoyin saka jari, inda aka yi kwaikwayon fitattun mutane irin su Aliko Dangote da Peter Obi suna ƙarfafa mutane su saka jari a wasu kamfanoni na bogi.

Mata ma ba su tsira ba, inda aka yi amfani da AI wajen ci musu zarafi a yanar gizo, musamman fitattun mata a siyasa, adabi, fina finai da nishaɗi, kamar yadda wasu suka yaɗa labarin cewa wata jarumar Kannywood, ta haihu ba tare da aure ba.

Haka kuma, an yi amfani da tsofaffin hotuna da bidiyo ana sake wallafa su kamar sabbin abubuwa, tare da danganta abubuwan da suka faru a wasu ƙasashe zuwa Najeriya.

Wajibi ne dai jama’a su riƙa tantance bayanai kafin yadawa, tare da dogaro da sahihan kafofi domin rage yaɗuwar labaran ƙarya a ƙasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here