Ya kamata a binciko musabbabin rasuwar ƴan majalisar dokokin Kano a rana guda–Dr. Bala Muhammad

0
15

Al’ummar Kano na cigaba da bayyana alhini bisa rasuwar ƴan majalisar dokokin jihar biyu a rana guda kuma a lokaci guda mai tazarar awa ɗaya.

Ƴan majalisar da suka rasu sune Hon. Aminu Sa’adu Ungogo, mai wakiltar ƙaramar hukumar Ungogo, wanda ya yi mutuwar fuj’a bayan kamuwa da rashin lafiya a harabar majalisar, sai Sarki Aliyu Daneji, na ƙaramar hukumar birni da ya rasu awa guda bayan rasuwar farko, biyo bayan gajeriyar rashin lafiya a asibiti. Mutuwar ta faru bayan tazarar awa guda a tsakani.

A kan hakan, Daily News 24 Hausa, ta zanta da masanin harkokin tarihi daga kwalejin ilimi ta Sa’adatu Rimi Kano, wato Dr. Bala Muhammad Inuwa Takai, don jin ko an taɓa ganin irin wannan rasuwa a tarihin Najeriya, wanda yace a masaniyar da yake da ita ba’a taɓa samun irin wannan rasuwar ƴan majalisar jiha guda a rana guda bayan tazara mara nisa ba. Ya jaddada cewa bai taɓa gamuwa da irin wannan lamari ba tsawon shekaru, duk da cewa babu abin da yafi ƙarfin ikon Allah.

Dr. Bala Muhammad, yace akwai bukatar mahukunta su gudanar da cikakken bincike don gano musabbabin rasuwar ƴan majalisar a lokaci guda, don fahimtar ko akwai wata matsalar da suka fuskanta wadda ta janyo rasuwar ko kuma rasuwa ce kamar yadda mutuwa ke samun sauran mutane.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here