Sarkin Kano na 15 ya miƙa saƙon taaziyyar rasuwar ƴan majalisar dokokin Kano

0
9

Sarkin Kano, na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero, ya bayyana alhini da jimami kan rasuwar ‘yan Majalisar Dokokin Jihar Kano guda biyu.

Ƴan majalisar sune Aminu Sa’adu Ungogo mai wakiltar ƙaramar hukumar Ungogo, da Hon. Sarki Aliyu Daneji mai wakiltar ƙaramar hukumar birnin Kano waɗanda suka rasu a ranar 24 ga Disamba, 2025 bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.

A cikin wata sanarwa da aka fitar mai ɗauke da sanya hannun Alhaji Aminu Babba Dan Agundi, Sarkin Dawaki Babba, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya bayyana rasuwar ‘yan majalisar biyu a lokaci guda a matsayin babban rashi mai girma ga Jihar Kano da al’ummar ta baki ɗaya. 

Ya ce mutuwar tasu ta zo ne a wani muhimmin lokaci da jihar ke ci gaba da buƙatar jajircewar shugabanni masu kishin jama’a da gaskiya.

Ya bayyana mamatan a matsayin wakilai nagari da suka sadaukar da kansu wajen bauta wa al’ummomin su, tare da nuna kishin ƙasa, gaskiya da ƙwazo wajen gudanar da ayyukan majalisa. Ya ƙara da cewa gudummawar da suka bayar za ta ci gaba da kasancewa abin tunawa a tarihin siyasar Jihar Kano.

Har ila yau Alhaji Aminu Ado Bayero, ya miƙa ta’aziyya ga Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, dukkan ‘yan majalisar, da kuma iyalan mamatan, tare da al’ummomin Ungogo da ƙaramar hukumar birnin Kano wanda lamarin ya shafa kai tsaye.

Ya kuma yi addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta musu kura-kuran su, Ya karɓi ayyukan alherin su, kuma Ya sanya su cikin Aljannatul Firdausi. 

Haka kuma, ya roƙi Allah Ya bai wa iyalan mamatan, abokan aikinsu da daukacin al’ummar Jihar Kano haƙuri, juriya da ƙarfin zuciya a wannan lokaci mai cike da jimami da alhini.

Sanarwar hakan ta samu sa hannun Sarkin Dawaki Babba, Alhaji Aminu Babba Dan-agundi, a madadin Alhaji Aminu Ado Bayero.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here