Kungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan mummunan harin ƙunar baƙin wake da aka kai a Masallacin Kasuwar Gomboru da ke Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.
Kungiyar ta bayyana harin a matsayin aiki na dabbanci, rashin imani da tausayi, wanda aka aikata da nufin razana jama’a da rusa zaman lafiya a yankin Arewa da Najeriya baki daya.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Shugaban kungiyar kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya fitar.
A cikin sanarwar, Gwamnan ya bayyana matukar alhinin sa bisa faruwar lamarin tare da mika ta’aziyyar sa ga Gwamnatin Jihar Borno, musamman Gwamna Babagana Umara Zulum, da al’ummar jihar baki daya, ciki har da iyalan wadanda suka rasa rayukansu da kuma wadanda suka jikkata.
Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana kai hari a wurin ibada a matsayin babban laifi ga dan Adam da kuma keta alfarmar addini, yana mai cewa irin wadannan ayyuka ba za su taba karya gwiwar al’umma ba.
Ya jaddada cewa yankin Arewa zai ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen yaki da ta’addanci da tsageranci ta hanyar hadin kai da goyon bayan hukumomin tsaro.
Har ila yau, Gwamnan ya yi kira ga jami’an tsaro da shugabannin gwamnati a Jihar Borno da kada su karaya ko su bari tsoro ya rinjaye su, yana mai cewa ‘yan ta’adda na amfani da tsoro wajen cimma muradun su.
Ya bukaci a kara karfafa kokarin da ake yi domin kawar da ta’addanci da dawo da zaman lafiya mai dorewa.
Gwamna Inuwa Yahaya ya kuma nemi a kara tsaurara matakan tsaro a wuraren ibada da wuraren taruwar jama’a, musamman a lokutan bukukuwa.
Ya tabbatar wa al’ummar Borno cikakken goyon bayan gwamnonin Arewa a kokarin da ake yi na kare rayukan fararen hula.
A karshe, ya yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta wa wadanda suka rasu Ya kuma saka su a Aljannatul Firdaus, Ya bai wa iyalansu hakuri, tare da bai wa wadanda suka jikkata cikakkiyar lafiya.
Kungiyar ta sake jaddada kudirinta na tabbatar da zaman lafiya, tsaro da hadin kan yankin Arewa.


