Boko Haram ce ta kai harin masallacin Maiduguri–Sojoji

0
8

Rundunar Sojin Najeriya ta tabbatar da cewa fashewar bam ɗin da ta auku a wani masallaci da ke jihar Borno a ranar Laraba, 24 ga Disamba, 2025, aikin wani ɗan kunar bakin wake ne da ake zargin yana da alaƙa da ƙungiyar Boko Haram.

Lamarin ya faru ne a Masallacin Al-Adum Juma’at da ke yankin kasuwar Gamboru a cikin Maiduguri, a lokacin da masu ibada ke gudanar da sallar Magariba.

Fashewar ta janyo asarar rayuka da kuma jikkatar mutane da dama.

Da yake bayani ga manema labarai a ranar Alhamis, kakakin Rundunar Operation Hadin Kai, Laftanar Kanar Sani Uba, ya ce binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa harin na kunar bakin wake ne da wani da ake zargin ɗan Boko Haram ne ya aiwatar.

A cewarsa, “Sakamakon binciken farko ya nuna cewa wani da ake zargin ɗan ta’adda ne daga Boko Haram ya tayar da na’urar fashewa, lamarin da ya yi sanadin mutuwar sa da kuma fararen hula biyu a wurin.”

Uba ya ƙara da cewa jami’an tsaro sun ɗauki matakin gaggawa bayan faruwar lamarin, inda suka haɗa kai da hukumomin ceto domin shawo kan lamarin da hana ƙarin asarar rayuka.

Ya bayyana cewa sojoji tare da rundunar ‘yan sanda masu kula da na’urorin fashewa (EOD), sauran hukumomin tsaro, gwamnatin jihar Borno da hukumar NEMA sun killace yankin domin tabbatar da tsaron jama’a.

Rundunar sojin ta ce an gaggauta kai waɗanda abin ya shafa zuwa Asibitin Gabaɗaya da kuma Asibitin Koyarwa na Maiduguri domin samun kulawar gaggawa. 

Rahotanni sun tabbatar da cewa mutane 32 sun jikkata, inda biyu daga cikin su suka rasu a asibiti, yayin da wasu biyu ke cikin mummunan hali. Sauran kuma suna samun kulawa.

Sojoji sun tabbatar wa da mazauna Maiduguri cewa an ƙara tsaurara sintiri da sa ido a birnin da kewaye, musamman a wannan lokaci na bukukuwa, tare da kira ga jama’a da su kasance masu lura da abubuwan da ka’iya zama masu haɗari da haɗa kai da jami’an tsaro domin kare rayuka da dukiyoyi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here