Za’a sauya tsarin cirar harajin Naira 50 bayan tura kuɗi ta banki

0
9

A sakamakon sabuwar dokar haraji ta 2025, bankin Polaris, ya sanar da abokan hulɗar sa sanar da cewa daga ranar 1 ga Janairu, 2026, cajin Naira 50, za’a sauya masa suna ETML zuwa Stamp Duty.

Bisa sabon tsarin, mai aikawa da kuɗi ne zai rika biyan wannan caji, ba wanda ya karɓi kuɗin ba kamar yadda aka saba a baya.

Hukumar bankin ta bukaci jama’a su lura da wannan sauyi domin shirya mu’amalolin su na kuɗi nan gaba.

Polaris, ya sanar da hakan cikin sakon da ya aike wa abokan hulɗar ta Imel.

Idan za’a iya tunawa idan aka tura wa mutum kuɗin da ya kai Naira dubu 10 zuwa sama za’a caje shi Naira 50.

Sai dai sabon tsarin zai bayar da damar cirar haraji daga wanda ya tura kudin ba wanda aka turawa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here