Nijeriya ta samu na’urar magance kansar mafitsara ba tare da yanka jikin mara lafiya ba

0
6

Nijeriya ta cimma wani babban tarihi a fannin kula da lafiyar maza, bayan shigo da sabuwar na’urar zamani mai amfani ƙirƙirarriyar basira wato AI wajen magance cutar dajin mafitsara dake damun maza, ba tare da tiyata ko raɗaɗi ba.

Wannan sabuwar fasaha, wacce ake kira HIFU, an fara amfani da ita a jihar Legas ƙarƙashin jagorancin Farfesa Kingsley Ekwueme, ƙwararren likita da ya samu horo a Birtaniya.

Masana sun bayyana samun wannan na’ura a matsayin wani muhimmin sauyi ga lafiyar maza a Nijeriya, musamman wajen maganin kansar mafitsara.

Farfesa Ekwueme ya bayyana cewa HIFU na aiki ne ta hanyar sanya ta kai tsaye zuwa wurin da cutar take, inda take hallaka ƙwayoyin cutar kawai.

Ya ce, wannan na’ura cikakkiya ce mai aiki da ƙirƙirarriyar basira basira. Da zarar an shigar da bayanin inda cutar take, tana tafiya domin magance ta.

A cewarsa, marasa lafiya na iya komawa gida a rana ɗaya bayan an yi musu magani, saboda ba’a yanka jikin mutum yayin amfani da sabuwar basirar.

“Babu ciwo, babu rauni. Ana iya yin maganin da safe, zuwa yamma ka koma gida lafiya,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here