Gwamnatin tarayya ta shigar da tuhume-tuhumen almundahanar kuɗaɗe guda 16 a gaban Kotun Tarayya da ke Abuja kan tsohon Ministan Shari’a Abubakar Malami (SAN), tare da ɗan sa Abubakar Abdulaziz Malami.
A cikin karar mai lamba FHC/ABJ/CR/700/2025, gwamnatin ta zargi Malami, ɗan sa da kuma Bashir Asabe, ma’aikaciyar kamfanin Rahamaniyya Properties, da ɓoye asalin kuɗaɗe da ake zargin an same su ta haramtacciyar hanya, daga shekarar 2018 zuwa 2025.
Gwamnatin ta ce ana zargin Malami da amfani da kamfanoni da asusun bankuna wajen ɓoye kuɗaɗe da suka haura biliyoyin naira, ciki har da kuɗin sayen kadarori masu tsada a Maitama, Jabi da Garki a Abuja, da kuma kuɗaɗen da aka rika biya ta asusun kamfanin Meethaq Hotels Ltd da wasu kamfanoni.
Haka kuma, gwamnatin ta ce an gano kadarori masu tsada sosai da ake zargin suna da alaƙa da tsohon Ministan.
Sai dai har zuwa yanzu, Abubakar Malami bai fito fili ya mayar da martani kan tuhumar ba.


