Wata gobara da ta tashi a daren Talata tayi ɓarna a kasuwar Terminus da ke jihar Filato, inda ta lalata kusan shaguna 25, kamar yadda shugabannin kasuwar suka tabbatar.
Shaidu sun ce jami’an kashe gobara daga Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya da ta Jihar Plateau sun kai ɗauki cikin gaggawa, lamarin da ya hana wutar yaɗuwa zuwa sauran sassan kasuwar.
Sakataren kasuwar, Zakari Sale, ya bayyana cewa gobarar ta tashi ne tsakanin ƙarfe 8 zuwa 9 na dare, inda ya ce asarar da aka samu ba ta kai ta sauran gobarar baya ba da aka yi ba.
Wannan lamari ya faru ƴan watanni bayan wata babbar gobara da ta auku a kasuwar cikin watan Afrilun 2025, wadda ta lalata fiye da shaguna 500, tare da asarar da ta haura Naira biliyan 1.
Hukumar Kula da Babbar Kasuwar ta tabbatar da faruwar gobarar a wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba, inda ta ce ba a samu asarar rai ba, kuma ana ci gaba da bincike don gano musabbabin gobarar.


