Bam ya tashi a cikin masallaci ana tsaka da yin Sallah a Maiduguri

0
12
Borno
Borno

Bam ya tashi a cikin masallaci ana tsaka da yin Sallah a Maiduguri–Vanguard

Wani abin fashewa da ake zargin an dasa a cikin wani masallaci da ke Kasuwar Gamboru a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, ya tashi da misalin ƙarfe 6:00 na yammacin Talata yayin da masu ibada ke tsaka da sallar Magariba.

Majiyoyi sun bayyana cewa masallacin na samun halartar dimbin jama’a, musamman ’yan kasuwa masu saye da sayarwa da ke harkokin su a kasuwar Gamboru a yau da kullum.

Jaridar Vanguard, ta rawaito cewa an jima ba’a fuskanci irin wannan harin wajen ibada a jihar Borno ba.

A halin da ake ciki, ba a samu jin ta bakin rundunar ’yan sandan jihar ba, domin samu wayar Jami’in hulɗa da Jama’a na rundunar ’yan sandan jihar Borno, ASP Kenneth Daso, ba har zuwa lokacin da ake kammala wannan rahoto.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here