Sanatoci biyu daga jihar Rivers Allwell Onyesoh daga mazaɓar Rivers ta Kudu maso Gabas da Mpigi Barinada na mazaɓar Rivers ta Yamma sun sanar da ficewar su daga jam’iyyar PDP zuwa APC.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ne ya bayyana hakan a zaman majalisar na ranar Talata bayan karanta wasiƙun sauya sheƙar da sanatocin suka aike wa majalisar.
A wasiƙar sa, Barinada ya ce ya yanke shawarar barin PDP bayan tattaunawa mai da al’ummar mazabar sa, yana mai cewa hakan ya dace da muradun su.
Shi kuma Onyesoh ya gode wa PDP da damar da ta ba shi ta farko har ya samu damar shiga Majalisar Dattawa.
Bayan sanarwar, Shugaban masu rinjaye a Majalisar Dattawa, Opeyemi Bamidele, ya ce doka ta tanadi dama ga duk wanda ke son shiga APC ba tare da nuna bambanci ba.


