Na yi nadamar goyon bayan Tinubu a zaɓen 2023—Makinde

0
7

Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana cewa yana cikin nadamar goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, inda ya ce abin bai haifar da sakamakon da ya yi fata ba.

Makinde ya faɗi hakan ne a ranar Talata yayin ganawa da ’yan jarida a fadar gwamnatin jihar Oyo da ke Ibadan.

Gwamnan na daga cikin gwamnonin PDP guda biyar (G5) da suka yi adawa da ɗan takarar jam’iyyar su, Atiku Abubakar, a wancan zaɓe, sakamakon rikicin rabon yankin da zai yi takara, inda suka ce ya dace a fito da ɗan kudu bayan mulkin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari na shekaru takwas.

Na goyi bayan shugaban ƙasa na yanzu ne saboda na yi tunanin zai gyara ƙasa kuma ya haɗa ƙwararru domin fuskantar matsalolin Najeriya, amma abin takaici, ba abin da muke gani ke nan ba, inji shi.

Haka kuma, Makinde ya bayyana cewa rikicin sa da ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya samo asali ne bayan Wike ya shaida wa Tinubu cewa zai “riƙe PDP” domin ya taimaka masa a zaɓen 2027 ba tare da amincewar sauran shugabannin jam’iyyar ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here