Masu garkuwa da ƴan Maulidi a Filato sun nemi Naira miliyan 42 kuɗin fansa

0
8

Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun nemi kuɗin fansa na naira miliyan 1.5 kan kowane mutum daga cikin fasinjoji 28 da suka sace a ƙauyen Zak, yankin Bashar na ƙaramar hukumar Wase a jihar Plateau.

An sace fasinjojin ne a daren Lahadi yayin da suke kan hanyar su ta zuwa bikin Mauludi a ƙauyen Sabon Layi, inda ’yan bindiga suka tare motar su, suka tafi da su tare da barin motar a wurin.

Wani ɗan uwan ɗaya daga cikin waɗanda aka sace, Ibrahim Musa, ya ce masu garkuwar sun kira iyalan fasinjojin suna matsa lamba a biya kuɗin fansa, tare da cewa mutanen suna cikin koshin lafiya.

Ya ƙara da cewa iyalan sun roƙi masu garkuwar saboda talauci, inda ya bayyana cewa da yawa daga cikin waɗanda aka sace matasa ne, kuma iyayensu ba za su iya tara irin wannan kuɗi ba.

Rundunar ’yan sandan jihar Plateau ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa ta fara bincike domin ganin an ceto waɗanda aka sace.

A halin da ake ciki, al’ummar yankin sun yi kira ga gwamnati da ta ƙara tsaurara matakan tsaro saboda yawaitar garkuwa da mutane, fashi da satar shanu a ƙaramar hukumar Wase.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here