Lambar NIN ce lambar harajin kowanne ɗan Najeriya—FIRS

0
14

Hukumar Tattara Haraji ta Kasa (FIRS) ta tabbatar da cewa Lambar Shaidar Ɗan Ƙasa (NIN) da Hukumar NIMC ke bayarwa, ita ce yanzu lambar haraji (Tax ID) ga dukkan ’yan Najeriya.

Hukumar ta bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin wayar da kan jama’a kan sabbin dokokin haraji.

FIRS ta sanar da hakan ne hanyar wallafa bayanin a shafin ta na X.

FIRS ta ce ba sai mutum ya nemi wata sabuwar lambar haraji ba, domin NIN ɗin sa ta riga ta zama lambar harajin sa kai tsaye. 

Haka kuma, kamfanoni da aka yi wa rijista ba za su ƙara neman lambar haraji ta daban ba, domin lambar rajistar CAC ita ce za ta kasance lambar harajin su.

Bayyana hakan na zuwa ne bayan da jama’a suka nuna damuwa kan sabbin dokokin haraji da ke buƙatar gabatar da lambar haraji wajen wasu mu’amaloli, ciki har da buɗe ko mallakar asusun banki.

Hukumar ta ce Dokar Gudanar da Haraji ta Ƙasa (NTAA) da za ta fara aiki daga Janairu 2026, ta tanadi amfani da lambar haraji a wasu muhimman mu’amaloli. 

Sai dai FIRS ta jaddada cewa wannan ba sabon tsari ba ne, domin tun daga shekarar 2019 ake amfani da shi, sai dai yanzu aka ƙara ƙarfafa shi.

FIRS ta ƙara da cewa sabon tsarin zai haɗa dukkan lambobin haraji da ake amfani da su a baya zuwa lamba guda ɗaya, domin sauƙaƙa tantance masu biyan haraji, hana maimaituwar biyan haraji, rage satar haraji, da tabbatar da adalci.

Hukumar ta kuma yi kira ga jama’a da su yi watsi da jita-jita, tana mai cewa sabbin dokokin harajin an tsara su ne domin sauƙi, gaskiya da inganta tattara haraji a ƙasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here