Jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi kira ga Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar Kano da ya gaggauta janye jami’an tsaron da ke gadin Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero a gidan Sarki na Nasarawa.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a matsayin babban baƙo na musamman a bikin ƙaddamar da rundunar tsaron unguwanni da gwamnatin jihar Kano ta kafa.
A cewar sa, Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi na II shi ne kaɗai halastaccen Sarkin Kano, yana mai jaddada cewa duk wani yunƙuri na sauya hakan ba zai samu karɓuwa ba.
Haka kuma, Kwankwaso ya yi Allah-wadai da matakin da ya ce an ɗauka na ajiye Alhaji Aminu Ado Bayero a gidan Sarki na Nasarawa, inda ya bayyana wurin da kalmar da ke nuna rashin dacewa da mutuncin sarautar Kano.


