Babbar Kotun tarayya dake Abuja ta bai wa tsohon Ministan Shari’a Abubakar Malami (SAN), belin wucin gadi a shari’ar da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ke yi da shi.
Alƙalin kotun, Mai Shari’a Bello Kawu, ne ya yanke hukuncin bayar da belin a ranar 23 ga Disamba, 2025, yayin sauraron ƙarar da aka shigar ƙarƙashin lamba M/17220/2025.
A cewar umarnin kotun, an bayar da belin ne bisa sharuddan da EFCC ta gindaya tun da farko, ciki har da miƙa fasfo ɗin sa na ƙasa da ƙasa da kuma tabbatar da belin ta hannun mutane da zasu tsaya masa.
Rahotanni sun nuna cewa Malami ya amince da dukkan sharuddan belin da aka gindaya masa.
An ɗage shari’ar zuwa ranar 5 ga Janairu, 2026, domin ci gaba da sauraron ƙarar.


