Jiragen yaƙin Amurka na tattara bayanan sirri da shawagi a Najeriya–Reuters
Rahotanni daga kamfanin dillancin labarai na Reuters sun nuna cewa Amurka ta fara amfani da jiragen sama na musamman domin sa ido da tattara bayanan sirri a wasu sassan Nijeriya tun daga ƙarshen watan Nuwamba.
Wannan mataki na zuwa bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar shigar da sojoji cikin Najeriya, bisa zargin da ya yi na cewa ƙasar ta kasa kare Kiristoci daga hare-hare.
Bayanan bin diddigin jiragen sama sun nuna cewa jiragen leƙen asirin, waɗanda wani kamfanin Amurka mai suna Tenax Aerospace ke sarrafawa, suna tashi ne daga Ghana, su ratsa sararin samaniyar Nijeriya kafin su koma Accra.
Masana harkokin tsaro sun bayyana cewa irin wannan zirga-zirga na nuni da ƙoƙarin Amurka na ƙara sa ido da sake ƙarfafa tasirin ta a yankin Afirka ta Yamma, musamman bayan janyewar sojojin ta daga Nijar a baya-bayan nan.
Wani jami’in tsaro na Nijeriya, wanda ya nemi a ɓoye sunan sa, ya ce an amince da wannan aiki ne bayan wata ganawa da aka yi tsakanin mai bawa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu, da manyan jami’an tsaron Amurka a ranar 20 ga Nuwamba.
Sai dai Pentagon ya ƙi yin cikakken bayani kan ainihin aikin jiragen, yayin da sojojin Nijeriya ma ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba.
Rahoton ya ce jiragen suna yin shawagi a samaniyar Nijeriya kusan kowace rana, lamarin da ke janyo muhawara kan tsaro, diflomasiyya da kuma ikon ƙasa.


