Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da rundunar tsaron unguwanni 

0
12

Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da sabuwar rundunar tsaro don kare unguwanni mai mutune 2,000, a wani biki da aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano.

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ne ya jagoranci ƙaddamar da tawagar tare da samun halartar manyan jami’an tsaron ƙasa reshen Kano.

An kafa rundunar ne domin taimakawa hukumomin tsaro wajen sa ido, kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da ƙarfafa tsaro a matakin unguwanni a faɗin jihar.

Bayanan da suka fito sun nuna cewa rundunar ta ƙunshi matasa da aka horas kan dabarun tsaro, tattara bayanan sirri, da kuma aiki tare da ’yan sanda da sauran jami’an tsaro domin hana aikata laifuka tun kafin su faru.

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa za a rarraba mambobin rundunar a ƙananan hukumomi daban-daban, inda za su mayar da hankali wajen kare kasuwanni, makarantu, unguwanni, da sauran muhimman wurare.

Ta jaddada cewa ƙaddamar da rundunar na daga cikin manyan matakan da take ɗauka na samar da zaman lafiya mai ɗorewa da kuma tabbatar da tsaron al’umma a faɗin jihar.

Gwamnatin ta kuma yi kira ga al’ummar Kano da su ba da cikakken haɗin kai tare da mara wa rundunar baya, domin ta samu nasara a aikin ta na kare lafiyar jama’a da tabbatar da zaman lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here