Bai kamata a riƙa zargin gwamnoni da aikata laifin cin hanci da rashawa ba–Radda

0
8

Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya yi kira ga ’yan Najeriya da su daina dora wa gwamnonin jihohi kaɗai alhakin tsadar rayuwa da ke addabar al’umma, yana mai cewa gwamnatin tarayya ce ke karɓar kaso mafi girma na kuɗaɗen shiga na ƙasa.

Gwamna Radda ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi RFI Hausa, inda ya ce tsarin rabon kuɗaɗen tarayya na barin jihohi da ƙananan hukumomi cikin matsin lamba, duk da yadda jama’a ke zargin su da mallakar mafi yawan kuɗin ƙasa.

A cewar sa, duk lokacin da aka samu matsin tattalin arziƙi, jama’a kan fi karkata wajen zargin gwamnonin jihohi da shugabannin ƙananan hukumomi, alhali kashi 52 cikin 100 na kuɗaɗen Asusun Tarayya na zuwa hannun gwamnatin tarayya, yayin da sauran kashi 48 cikin 100 ake rabawa jihohi 36 da ƙananan hukumomi 774.

“Idan aka raba kuɗaɗen shiga, gwamnatin tarayya ce ke karɓar kaso mafi yawa. Don haka ya dace ’yan Najeriya su fara tambaya: ina ne yawancin kuɗaɗen nan suke tafiya?” in ji gwamnan.

Gwamna Radda ya kuma yi watsi da zargin da ake yi wa gwamnonin jihohi na cin hanci, yana mai cewa bai dace a yi wa dukkan shugabanni hukunci iri ɗaya ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here