An samu ƙaruwar man fetur da ƴan Najeriya ke amfani da shi a kowacce rana–NMDPRA

0
12
man fetur
man fetur

Hukumar kula da harkokin man fetur ta ƙasa (NMDPRA) ta bayyana cewa wadatar man fetur a Najeriya ta ƙaru da kashi 55 cikin 100 a watan Nuwamban 2025.

Rahoton hukumar ya nuna cewa ana rarraba lita miliyan 71.5 na man fetur a kullum a watan Nuwamba, idan aka kwatanta da lita miliyan 46 a watan Oktoba.

Haka kuma, yawan man da ’yan ƙasa ke amfani da shi ya ƙaru da kashi 44.5 cikin 100, inda ake shan lita miliyan 52.1 a kullum, daga lita miliyan 28.9 da aka samu a watan Oktoba.

NMDPRA ta ce ƙarin wadatar man ya samo asali ne daga shigo da man fetur da Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPC) ya yi, domin tara isasshen mai da kuma tabbatar da wadatar man a lokacin bukukuwan ƙarshen shekara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here