Fadar Shugaban Ƙasa ta ƙara kasafin kuɗin ƙasar nan na shekarar 2026 daga tiriliyan ₦54.46 zuwa tiriliyan ₦58.18 domin ɗaukar sabbin jami’an tsaro a rundunar soji, ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ne ya bayar da umarnin ƙarin ɗaukar ma’aikata a hukumomin tsaro, lamarin da ya sa aka ƙara kasafin kuɗin domin biyan albashi da sauran buƙatun da ke tattare da hakan.
Babban Daraktan Ofishin Kasafin Kuɗi na Ƙasa, Malam Tanimu Yakubu, ne ya bayyana sabon adadin bayan taron Majalisar Zartarwa ta Ƙasa da aka gudanar a ranar Juma’a, kafin Shugaban Ƙasa ya miƙa kasafin gaban Majalisar Dokoki.
Wata majiya daga fadar shugaban ƙasa ta ce tuni ma’aikatun gwamnati suka kammala miƙa buƙatun kasafin su, amma ƙarin ɗaukar jami’an tsaro ya tilasta sake duba kasafin gaba ɗaya.
Majiyar ta ƙara da cewa ba a tattauna cikakkun bayanan kasafin ba a taron majalisar zartarwar, domin lokaci ya ƙure, sai aka garzaya da miƙa kasafin ga majalisa domin nuna ƙudurin gwamnati na ganin an amince da shi da wuri.


