Gwamnatin tarayya ta sanar da kafa wata dokar da ta wajabta yin gwajin ta’ammali da miyagun ƙwayoyi ga duk wanda ke neman shiga aikin gwamnati a faɗin ƙasar nan.
An bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da aka aikewa manyan sakatarorin ma’aikatu da shugabannin hukumomin gwamnati, inda aka umurce su da aiwatar da sabon tsarin kafin ɗaukar sababbin ma’aikata.
Daraktan yaɗa labarai na ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Segun Imohiosen, ya ce matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na dakile yawaitar shaye-shayen ƙwayoyi, musamman a tsakanin matasa, wanda ke barazana ga ci gaban ƙasa da tsaro.
Ya bayyana cewa matsalar shaye-shaye na da illa ga lafiyar al’umma, tattalin arziƙi, aikin ofisoshi da tsaron ƙasa baki ɗaya.
A cewarsa, an umurci ma’aikatu da hukumomin gwamnati da su yi aiki tare da Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa, domin gudanar da gwajin bisa ƙa’idojin da aka tanada.


