Hukumar kula da gidajen gyaran hali ta jihar Kano ta kama wasu mata biyu da ake zargi da yunƙurin shigar da miyagun ƙwayoyi gidan gyaran hali na Goron Dutse da ke birnin Kano.

Kakakin hukumar a jihar Kano, CSC Musbahu Lawan Ƙofar Nassarawa, ne ya tabbatar da faruwar lamarin ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, 22 ga Disamba, 2025.
A cewar sa, an kama matan ne a lokacin da suke ƙoƙarin shiga gidan gyaran halin ɗauke da miyagun ƙwayoyi da suka ɓoye a cikin gurasa, tare da wasu kayayyaki da suka saɓa wa dokokin hukumar.
Musbahu ya bayyana cewa matan guda biyu na da shekaru tsakanin 19 zuwa 20, kuma duka mazauna jihar Kano ne.
Ya ce jami’an hukumar sun gano shirin nasu yayin binciken tsaro da ake yi kafin ba wa baƙi damar shiga gidan gyaran hali.
Ya ƙara da cewa wannan nasara ta nuna jajircewar hukumar wajen kare lafiyar mazauna gidajen gyaran hali, tare da hana shigar da duk wani abu da ka iya cutar da su ko karya doka.
A halin yanzu, hukumar ta miƙa matan biyu ga Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), reshen jihar Kano, domin ci gaba da bincike da ɗaukar matakin da doka ta tanada.


