Ɗaliban jami’ar Northwest sun koka kan jinkirin basu shaidar kammala karatu

0
11

Wasu daga cikin ɗalibai da suka kammala karatu a Jami’ar Northwest da ke Kano sun nuna damuwar su kan jinkirin fitar da takardun shaidar kammala karatun su wato (certificate), lamarin da suka ce ya daɗe yana hana su ci gaba da karatu ko samun damar aiki musamman a ƙasashen waje.

Wani tsohon ɗalibi da ya kammala karatu a shekarar 2020 ya shaidawa Daily News 24, cewa har yanzu ba a ba shi takardar shaidar kammala karatu ba, illa takardar sakamako (statement of result) kaɗai, abin da ya ce ya kawo masa cikas wajen neman gurbin karatu na gaba.

Haka zalika wata tsohuwar ɗaliba ta bayyana cewa duk da kammala dukkan sharuddan karatu, itama bata karɓi takardar ta ba, yayin da wasu ke cewa har ma takardar sakamako ba su samu ba.

Da yake martani kan koken, Jami’in hulɗa da jama’a na jami’ar, Abubakar Ibrahim, ya bayyana cewa jinkirin ya samo asali ne sakamakon kura-kuran da aka gano yayin buga takardun shaidar kammala karatun ɗaliban inda aka sanya wasu bayanai ba su dace da sahihiyar amincewar jami’ar ba.

Ya ce tuni an gyara wasu daga cikin takardun, kuma an kawo su daga ƙasar Birtaniya, inda ake ajiye su a ofishin maga-takardan jami’ar (Registrar) domin fara karɓa. Ya ƙara da cewa kamfanin da ya buga takardun ya amince da laifin da ya yi.

Abubakar Ibrahim ya kuma bayyana cewa an kammala takardun shaidar digiri na shekarar 2023/2024 da digiri na shekarar 2022/2023, kuma za a fara bayarwa daga yau Litinin, 22 ga Disamba, 2025, daga ƙarfe 10 na safe zuwa 4 na yamma, ranakun Litinin zuwa Juma’a.

Ya buƙaci ɗalibai su riƙa karɓar sahihin bayani daga jami’an jami’a kaɗai, tare da ba da haƙuri ga waɗanda har yanzu ba a kammala nasu ba, yana mai cewa jami’ar na ɗaukar matakan gaggawa domin kawo ƙarshen matsalar gaba ɗaya.

Duk da haka, wasu daga cikin tsofaffin ɗaliban sun bayyana fatan cewa wannan yunƙuri zai kawo mafita ta dindindin, domin su samu damar ci gaba da rayuwa ta ilimi da aiki ba tare da cikas ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here