Ƙungiyar NIPR ta sanya lokacin zaɓen sabbin shugabanni

0
8

Ƙungiyar Masana Harkokin Hulɗa da Jama’a ta Nijeriya (NIPR) reshen Jihar Kano ta ayyana ranar 31 ga Janairu, 2026 domin gudanar da babban taron ta na shekara tare da zaɓen sababbin shugabanni.

An yanke wannan matsaya ne a ƙarshen taron majalisar zartarwar ƙungiyar ta jiha da aka gudanar a ranar Lahadi, bayan karewar wa’adin shugabannin da ke kan mulki.

Shugaban kungiyar na Kano, Aliyu Yusuf, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a yau.

A cewar sanarwar, ƙungiyar ta kafa kwamitin zaɓe mai mutum biyar domin shiryawa tare da gudanar da zaɓen sabbin mambobin majalisar zartarwa a yayin taron.

Malam Aminu Hamza ne shugaban kwamitin, yayin da Musbahu Aminu Yakasai ke matsayin sakatare. Sauran mambobin sun haɗa da Malam Aminu Inuwa, Farfesa Mainasara Yakubu Kurfi da Uba Abdullahi.

Haka kuma, an kafa kwamitin shirya taro mai mutum goma sha biyar, inda Aliyu Yusuf ke jagorantar kwamitin, yayin da Usman Gwadabe ke matsayin sakatare.

Kwamitin zai kula da dukkan shirye-shirye da tafiyar da taron shekara gaba ɗaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here