Sojoji sun daƙile jigilar kayayyaki ga mayaƙan Boko Haram da ISWAP

0
11

Dakarun Rundunar Sojin ƙasa sun dakile yunkurin kai kayayyakin tallafi zuwa ga mayaƙan Boko Haram da ISWAP a jihar Borno.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne aka samu nasarar kama kayan a kan hanyar Maiduguri zuwa Bama, inda sojojin suka kama wata mota ɗauke da kayan abinci da abubuwan sha da ake zargin an tanadevsu ne domin ƴan ta’adda.

Kakakin rundunar Operation Hadin Kai, Laftanal Kanal Sani Uba, ya bayyana cewa a wani aikin sintiri da aka gudanar a ranar 17 ga Disamba, sojoji sun gano wani bam da aka binne a kan hanyar Damboa–Komala. Ya ce an tabbatar da tsaron yankin bayan kwance bam ɗin tare da tarwatsa shi.

Haka zalika sojojin sun kama mutum biyu da ake zargi da hannu a lamarin, tare da ƙwato kayayyaki da suka haɗa da wayoyin salula, katin shaida, zobe, da kuɗaɗen Naira da CFA.

An miƙa waɗanda ake zargin, motar da kuma kayayyakin da aka ƙwato ga sashen leƙen asirin soji domin ci gaba da bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here