ICPC Ta Gayyaci Dangote Kan Zargin Tsohon Shugaban NMDPRA Da Almundahana

0
9

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da Dangogin su ta Ƙasa (ICPC) ta gayyaci attajirin ɗan kasuwa, Aliko Dangote, domin bayyana a gaban wani kwamitin bincike na musamman a Abuja, biyo bayan ƙarar da ya shigar kan tsohon shugaban Hukumar Kula da Harkokin Sarrafawa da tace Man Fetur (NMDPRA), Ahmed Farouk.

Wata majiya daga cikin ICPC ta tabbatar da cewa hukumar ta kafa kwamitin manyan masu bincike domin duba ƙarar da Dangote ya gabatar, kuma shugaban hukumar, Dr. Musa Aliyu (SAN), ya umarci a ba wa batun kulawa ta musamman.

Ana sa ran Dangote zai halarci zaman binciken da kansa ko kuma ya tura lauyan sa, Ogwu Onoja (SAN), tare da hujjojin da ke goyon bayan zargin, yayin da ICPC ke fara bincike a hukumance.

A cikin ƙarar, Dangote ya zargi Farouk da cin hanci da almundahana, ciki har da kashe sama da dala miliyan bakwai wajen biyan kuɗin karatun ‘ya’yansa huɗu a manyan makarantu masu tsada a ƙasar Switzerland, ba tare da hujjar halalcin kuɗin da ya kashe ba.

Har ila yau, Dangote ya ce tsohon shugaban NMDPRA ya taimaka wajen raunana harkar tace mai a cikin gida, ta hanyar haɗin baki da ‘yan kasuwar ƙetare da masu shigo da mai, inda ya ci gaba da bayar da lasisin shigo da mai daga waje.

Ko da yake Ahmed Farouk ya yi murabus daga muƙaminsa, ICPC ta bayyana cewa hakan ba zai hana ci gaba da bincike ba, tana mai jaddada cewa murabus ba kariya ba ne daga binciken doka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here