Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa an samu nasarar kuɓutar da ɗalibai 130 da wasu ’yan bindiga suka sace daga makarantar St. Mary’s Firamare da Sakandare da ke Papiri, a Jihar Neja.
Mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, Sunday Dare, ne ya tabbatar da hakan a ranar Lahadi ta shafinsa na X, inda ya ce an kuɓutar da dukkan yaran da aka sace ba tare da barin kowa a hannun masu garkuwa ba.
Sanarwar ta zo ne tare da hoton yaran da aka kuɓutar, wanda ke nuna cewa dukkansu sun samu ’yanci bayan harin da aka kai makarantar.
Ana sa ran fitar da ƙarin bayani kan lamarin nan gaba kaɗan.


