Tinubu ya yi barazanar fara turawa ƙananun hukumomi kuɗin su kai tsaye

0
14
Tinubu

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci gwamnoni da su mutunta umarnin Kotun Ƙoli da ya bai wa ƙananan hukumomi damar karɓar kuɗaɗen su kai tsaye ba tare da katsalandan ba.

Tinubu ya gargaɗi gwamnonin da ke ƙoƙarin ƙin bin umarnin kotun, yana mai cewa idan suka ci gaba da yin watsi da hukuncin, zai tilasta aiwatar da wata doka da za ta ba shi ikon aikewa ƙananan hukumomi kuɗaɗen su kai tsaye daga asusun rabon arzikin tarayya.

Shugaban ƙasar ya yi wannan gargaɗi ne yayin taron majalisar zartarwar jam’iyyar APC karo na 15 da aka gudanar a birnin Abuja.

Ya ce Kotun Ƙoli ta riga ta yanke hukunci a bayyane, inda ta umarci jihohi da su daina riƙe kuɗaɗen ƙananan hukumomi.

 Tinubu ya jaddada cewa yana mutunta gwamnoni, amma ba zai lamunci take doka ba.

A ranar 11 ga Yulin 2024 ne Kotun Ƙoli ta tabbatar da cewa riƙe kuɗaɗen ƙananan hukumomi da jihohi ke yi ya saɓa wa kundin tsarin mulkin Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here