Gwamnatin Kano ta ware Naira biliyan 26 don ayyukan raya ƙasa

0
10

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da kashe jimillar kuɗi har ₦26.1 biliyan domin aiwatar da ayyukan gina hanyoyi, samar da ruwan sha da kuma biyan diyya ga al’ummar jihar.

Bayanin hakan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya wa hannu a ranar Asabar.

Sanarwar ta bayyana cewa an yanke wannan matsaya a taron Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano karo na 35, wanda aka gudanar a ranar 18 ga Disamba, 2025.

Daga cikin manyan ayyukan da aka amince da su, akwai ₦16.29 biliyan domin sake bayar da kwangilar gina hanyar Gwarzo–Tsaure–Tsanyawa, yayin da aka ware ₦6.81 biliyan domin biyan diyya ga masu kadarori 5,015 na yankin Rimin Zakara.

Haka kuma, an amince da kashe ₦2.22 biliyan domin gyaran hanyar Murtala Mohammed Way da sauran hanyoyin da ke kusa da ita.

A ɓangaren samar da ruwan sha, gwamnan ya amince da ₦398.2 miliyan domin aiwatar da mataki na biyu na Ayyukan Samar da Ruwan Sha na Abba Kabir Yusuf Reach-Out, da kuma ₦182.1 miliyan don faɗaɗa layin bututun ruwan Hotoro.

Bugu da ƙari, an ware ₦111.7 miliyan domin gyaran Madatsar Ruwa ta Gani Earth Dam.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa wadannan ayyuka na da nufin inganta zirga-zirga, sauƙaƙa samun ruwan sha mai tsafta, da bunƙasa harkokin tattalin arziki a fadin Jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here