Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da daftarin kasafin kuɗin shekarar 2026, wanda ya kai N58.18 tiriliyan, a gaban zaman haɗin gwiwa na Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai a Abuja, inda biyan bashin zai ɗauki Naira triliyan 15.52 wato kusan kashi 26.7% na jimillar kasafin.
Kasafin, wanda aka sanya masa suna “Kasafin Ƙarfafa Gyare-gyare, Sabunta Juriya da Rabon Arziki ga Kowa”, ya nuna cewa kudin shiga da gwamnati ke sa ran samu a 2026 ya kai Naira triliyan 34.33, yayin da gibin kasafi ya kai Naira triliyan 23.85.
Tinubu ya amince cewa nauyin biyan bashi na matsa wa kasafin Najeriya, amma ya ce gwamnati na jajircewa wajen tabbatar da tsarin kuɗi mai ɗorewa, gaskiya da amfani da kuɗi yadda ya dace.


