Majalisa Ta Yi Watsi da Ƙudirin Hukunta Masu Sayen Kuri’a a Zaɓen Fidda Gwani

0
7

Majalisar Wakilai ta ƙi amincewa da wani ƙudiri da ke neman haramta siyan kuri’a a lokacin zaɓen fidda gwani na jam’iyyun siyasa.

Ƙudirin ya zo ne a yayin nazarin gyaran Dokar Zaɓe ta 2022 sashi zuwa sashi, inda aka gabatar da tanadin da ke cewa duk wanda ya ba wa wakili (delegate) kuɗi ko wani abu domin rinjayar sakamakon zaɓen jam’iyya, zai fuskanci hukuncin ɗaurin shekaru biyu a gidan yari ba tare da zaɓin tara ba.

Sai dai ‘yan majalisar sun ƙi amincewa da wannan sashe baki ɗaya, bayan mataimakin kakakin majalisar, Benjamin Kalu, ya nemi kuri’ar murya a zaman ranar Alhamis.

Masu sharhi a fannin siyasa sun bayyana cewa sayar da kuri’ar wakilai ya zama ruwan dare a zaɓukan jam’iyya a Najeriya, musamman saboda tsarin da ke bai wa ƙananan wakilai ikon yanke hukunci kan sakamakon zaɓe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here