Majalisar Wakilai ta ƙara adadin kuɗaɗen da za’a yi amfani dasu wajen gudanar da yaƙin neman zaɓe a faɗin ƙasa.
Majalisar ta amince da ƙara kuɗin yaƙin neman zaɓe na shugaban ƙasa daga Naira biliyan 5 zuwa Naira biliyan 10, sannan na Gwamna daga Naira biliyan 1 zuwa Naira biliyan 3.
Hakan na cikin ƙudirin gyaran Dokar Zaɓe 2025 da Majalisar ta amince da shi.
Haka kuma, Majalisar ta wajabta wa INEC ta rika tura sakamakon zaɓe kai tsaye zuwa dandalin tattara sakamakon zaɓen daga kowace rumfar zaɓe.
Ƙarin kuɗin kamfen ga sauran kujeru
Sanata: daga Naira miliyan 100 zuwa Naira miliyan 500.
Dan Majalisar Wakilai: daga Naira miliyan 70 zuwa Naira miliyan 250.
Majalisar Jiha: daga Naira miliyan 30 zuwa Naira miliyan 100.
Shugaban Karamar Hukuma: daga Naira miliyan 30 zuwa Naira miliyan 60.
Kansila: daga Naira miliyan 5 zuwa Naira 10.
An kuma iyakance gudummawar mutum ko kamfani ga ɗan takara zuwa Naira 500m kacal.


