Tinubu zai gabatar da kasafin kuɗin 2026 a  gobe Juma’a 

0
9

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai gabatar da Kasafin Kuɗi na shekarar 2026 ga zaman haɗin gwiwar Majalisar Dattawa da ta Wakilai a gobe Juma’a da ƙarfe 2:00 na rana.

Ofishin Maga takardan Majalisar Ƙasa ya sanar da cewa an nemi duk masu ruwa da tsaki su kasance a wuraren aikin su tun daga 11:00 na safe, domin tsaurara matakan tsaro kafin shigowar shugaban ƙasa zauren majalisar.

Rahotanni sun nuna cewa kasafin na 2026 zai kai naira tiriliyan 54.4.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here