Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da sake fasalin Hukumar Kula da Harkokin Wutar Lantarki ta Ƙasa (NERC), da mambobin hukumar a ranar 16 ga Disamba, 2025.
A cikin sanarwar da mai bawa shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu ya buƙaci sabbin mambobin NERC su ƙarfafa sauye-sauyen da ake yi a ɓangaren wutar lantarki, bisa tanadin Dokar Wutar Lantarki ta 2023.
Sabbin mambobin kwamitin NERC sun haɗa da:
Dr. Mulisiu Olalekan Oseni — Shugaba
Dr. Yusuf Ali — Mataimakin Shugaba
Nathan Rogers Shatti — Kwamishina
Dafe Akpeneye — Kwamishina
Aisha Mahmud Kanti Bello — Kwamishina
Dr. Chidi Ike — Kwamishina
Dr. Fouad Animashaun — Kwamishina
Nadin Dr. Oseni ya fara aiki daga 1 ga Disamba, 2025, kuma zai cika wa’adin shekaru goma a hukumar, kamar yadda doka ta tanada.


