Majalisar Dattawa ta amince da naɗin sunayen mutane 64 a matsayin Jakadu.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ne ya miƙa sunayen, ciki har da tsohon Ministan Harkokin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode, da tsohon mai bawa shugaban ƙasa shawara, Reno Omokri.
Amincewar ta biyo bayan gabatar da rahoton Kwamitin Harkokin Waje na Majalisar, wanda ya ce an tantance dukkan waɗanda aka naɗa tare da tabbatar da cewa sun cancanta.
Hakan ya zo kwanaki biyu bayan Majalisar ta amince da wasu jakadu uku, lamarin da ya kai adadin jakadun da aka amince da su zuwa 67.
Daga cikin waɗanda aka tantance akwai tsohon Ministan Cikin Gida, Abdulrahman Dambazau; tsohon shugaban INEC, Mahmood Yakubu; tsohon gwamnan Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi; da tsohon gwamnan Abia, Okezie Ikpeazu.


