Wata babbar kotun tarayya dake Abuja ta ƙi amincewa da buƙatar bayar da belin tsohon Ministan Shari’a Abubakar Malami, ya gabatar.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Babangida Hassan, ya ce ba zai iya bayar da belin Malami ba, domin wata kotu mai matsayi iri ɗaya da tass riga ta bai wa EFCC umarnin tsare Malami don ci gaba da bincike.
Rahotanni sun nuna cewa Malami na hannun EFCC tun makon jiya, bisa zargin almubazzaranci da kuɗaɗen al’umma.
Lauyan tsohon ministan, Sulaiman Hassan (SAN), ne ya nemi belin, yana mai cewa tsare Malami ba bisa ka’ida ba.
Sai dai lauyan EFCC, Jibrin Okutepa (SAN), ya tabbatar wa kotu cewa ana tsare da shi ne bisa sahihin umarnin kotu.


