Gwamnatin tarayya ta sake buɗe makarantu 47 da ta rufe saboda rashin tsaro 

0
9

Gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin sake buɗe dukkan makarantu 47 na haɗaka da aka rufe sakamakon matsalolin tsaro.

A wata sanarwa da Daraktar Hulɗa da Jama’a ta Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Boriowo Folasade, ta fitar, ta ce an ƙarfafa tsarin tsaro a ciki da wajen makarantu, lamarin da ya bawa gwamnati damar tabbatar da lafiyar ɗalibai da malamai.

Sanarwar ta bayyana cewa tuni ɗalibai suka koma makarantu, inda wasu ke kammala shirye-shiryen karatu na watan Disamba, yayin da wasu kuma suka kammala jarabawar su cikin nasara.

Gwamnati ta bai wa iyaye da jama’a tabbacin cewa lafiya, walwala da tsaron ɗalibai na daga cikin manyan abubuwan da take bai wa muhimmanci, tare da haɗin gwiwa da hukumomin tsaro domin ci gaba da samar da kwanciyar hankali a makarantu faɗin ƙasar.

Ta kuma jaddada cewa kare haƙƙin kowane yaro na samun ilimi a yanayi mai tsaro na daga cikin manufofin gwamnatin tarayya, tare da ƙudurin hana duk wata tangarda ga jadawalin karatu.

Idan za’a iya tunawa a ranar 21 ga Nuwamba, 2025, Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta bayar da umarnin rufe makarantu 47 na Unity Schools sakamakon barazanar hare-haren tsaro a wasu sassan ƙasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here