Ƴan sanda sun kama dillalin tabar Wiwi a birnin Kano

0
12

Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi tare da kwace adadi mai yawa na ganyen da ake zargin tabar wiwi ce.

A cewar wata sanarwa da rundunar ta fitar, kamen ya biyo bayan ci gaba da gudanar da wani bincike da aka fara tun bayan wani sintiri da aka gudanar kan wasu da ake zargin masu fashi da makami ne. 

Ibrahim Mohammed, shi ne wanda ake zargi da safarar inda ya kasance mazaunin unguwar Rijiyar Zaki. An samu nasarar kama shi a ranar 15 ga Disamba, 2025.

Rundunar ta ce an kwato buhuna huɗu da fakiti 297 na busassun ganye da ake zargin wiwi ne daga hannun wanda ake zargin a lokacin da aka kama shi.

Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da aikin bisa jajircewa da ƙwarewa. Ya kuma bayar da umarnin a kammala binciken cikin gaggawa domin gurfanar da wanda ake zargi da duk wasu abokan aikin sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here