Majalisar Wakilai ta soma bincike kan zargin cewa an sauya wasu sassan dokokin haraji da majalisar ta amince da su, bayan an fitar da su domin jama’a su gani.
Ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Sokoto ta Kudu, Hon. Abdulsammad Dasuki daga jam’iyyar PDP, ne ya bankaɗo batun a zaman majalisar na ranar Laraba.
Dasuki ya bayyana cewa an tauye haƙƙin sa na ɗan majalisa, inda ya ce abubuwan da aka wallafa a dokokin harajin ba su yi daidai da abin da ‘yan majalisa suka tattauna, suka kada ƙuri’a, kuma suka amince da shi ba.
“Na halarci zaman majalisar, na kada ƙuri’a ta kuma an ƙirga ta, amma abin da nake gani a yanzu ya bambanta gaba ɗaya,” in ji Dasuki.
Dasuki ya yi gargaɗin cewa barin dokokin da ba su dace da abin da majalisa ta amince da shi ba su shiga hannun ‘yan Najeriya zai tauye mutuncin majalisa tare da karya kundin tsarin mulki.
Da yake mayar da martani, Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Abbas Tajudeen, ya ce ya lura da ƙorafin da aka gabatar, kuma ya tabbatar wa majalisa cewa za a ɗauki matakan da suka dace domin magance batun.


