ICPC za ta binciki zargin Dangote kan Shugaban NMDPRA

0
7

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da dangogin su ta ƙasa (ICPC) ta tabbatar da karɓar ƙorafi daga Alhaji Aliko Dangote, inda ya zargi Shugaban Hukumar Kula da Albarkatun Man Fetur ta  Ƙasa (NMDPRA), Farouk Ahmed, da aikata almundahana.

Dangote ya yi zargin cewa Farouk Ahmed ya kashe dala miliyan biyar da aka ce kuɗin karatun ’ya’yansa ne a makarantu da ke ƙasar Switzerland. 

Haka kuma, ya zarge shi da aikata lalata tattalin arziƙi, inda ya miƙa ƙorafin ga ICPC domin ta bincika.

A wata sanarwa da kakakin ICPC, John Odey, ya fitar a ranar Talata, ya ce hukumar ta karɓi ƙorafin a hukumance a ranar 16 ga Disamba, 2025, ta hannun lauyan Dangote.

Sanarwar ta ce: “ICPC ta tabbatar da karɓar ƙorafi daga Alhaji Aliko Dangote kan Shugaban NMDPRA, Alhaji Farouk Ahmed. Hukumar za ta binciki lamarin yadda ya dace.”

ICPC ta jaddada aniyar ta ta gudanar da cikakken bincike kan zargin domin tabbatar da gaskiyar lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here