Binciken ICPC ne zai bayyana gaskiya a kan zargin da Dangote ke yi min–Shugaban NMDPRA

0
5

Shugaban Hukumar Kula da Albarkatun Man Fetur ta ƙasa (NMDPRA), Farouk Ahmed, ya bayyana cewa zargin da shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya yi masa wata dama ce da za ta ba shi damar kare kansa da kuma fayyace gaskiya ta hanyar binciken hukuma.

A wata sanarwa da NMDPRA ta fitar, Ahmed ya ce yana maraba da duk wani bincike na gaskiya, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen nazartar dukkan bayanai ba tare da son zuciya ba.

Ya bayyana cewa ba zai shiga ce-ce-ku-ce a kafafen yaɗa labarai ba, duk da zarge-zargen da ake yi masa, yana mai jaddada cewa hanyar doka da tsarin bincike su ne mafi dacewa wajen warware takaddamar dake tsakanin sa da Dangote.

Ahmed ya kuma nanata cewa hukumar da yake jagoranta tana bin doka da ƙa’idoji a dukkan ayyukan ta, tare da ƙudirin tabbatar da gaskiya, adalci da kuma ƙarfafa tsarin kula da harkokin man fetur a Najeriya.

A halin da ake ciki, Hukumar ICPC ta sanar a ranar Talata cewa za ta gudanar da bincike kan zargin da Aliko Dangote ya shigar kan shugaban NMDPRA, dangane da almundahanar kuɗaɗe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here