Ahmed Musa ya yi ritaya daga bugawa Najeriya ƙwallo

0
11

Fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafa kuma tsohon kyaftin ɗin Super Eagles, Ahmed Musa, ya sanar da yin ritaya daga buga wa Najeriya ƙwallo.

Ahmed Musa ya bayyana wannan mataki ne ta cikin wani saƙon da ya wallafa a shafin sa na X, inda ya gode wa ’yan Najeriya bisa goyon bayan da suka ba shi tun daga farkon rayuwar sa har zuwa yau.

Musa, wanda shi ne ɗan wasan Najeriya mafi yawan buga wasa a tarihin ƙasa da wasanni 111, ya ce bayan dogon tunani ya yanke shawarar ajiye buga wa ƙasar wasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here