Ƙarancin iskar gas ya janyo ƙarancin wutar lantarki a faɗin Najeriya

0
8

Akwai barazanar ‘yan Najeriya su gudanar da bukukuwan Kirsimeti ba tare da isashshsiyar wutar lantarki ba, idan har Gwamnatin Tarayya ba ta ɗauki matakin gaggawa wajen biyan bashin kuɗaɗen iskar gas da ake amfani da ita wajen samar da wuta ba. 

Rahotanni sun nuna cewa kamfanonin gas sun fara rage isar da gas ga tashoshin samar da lantarki, lamarin da ke shafar samar da wuta a faɗin ƙasar.

A ranar Talata, Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Enugu (EEDC) ya sanar da abokan hulɗar sa a jihohin Kudu maso Gabas game da wannan matsala ta hanyar wata sanarwa da Shugaban Sadarwa na kamfanin, Emeka Ezeh, ya fitar.

EEDC ya bayyana cewa raguwar wutar lantarki da ake samu na faruwa ne sakamakon ƙarancin iskar gas da ke shafar kamfanonin samar da wuta, wanda ya haifar da raguwar wutar lantarki da ake tattarawa. 

Kamfanin ya nemi afuwar abokan hulɗar sa, yana mai jaddada cewa ana ƙoƙarin daidaita lamarin domin dawo da ingantacciyar wutar lantarki ga al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here