Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana aniyar gwamnatin sa ta ci gaba da aiwatar da manufofi da ayyukan marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, yana mai jaddada cewa za su ɗora daga inda ya tsaya.
Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a Abuja, yayin bikin ƙaddamar da littafin tarihin rayuwar Buhari wanda Dr. Charles Omole ya rubuta. A cewar sa, mafi girman girmamawa da za a iya yi wa marigayi Buhari ita ce tabbatar da dorewar ayyukan shugabancin sa domin amfanin ƙasa.
Tinubu ya ce littafin ya yi cikakken bayani kan rayuwar Buhari, inda ya nuna nasarorin sa da kuma kura-kuran sa cikin adalci, tare da ƙarfafa shugabanni masu zuwa su ɗauki darussa daga tarihin rayuwar tasa.
A wajen taron, Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya yabawa Shugaba Tinubu bisa tsayawa tare da iyalan Buhari da al’ummar Katsina, yana mai bayyana marigayin a matsayin mutum mai ladabi, kishin ƙasa da nagartaccen shugabanci.
Shi ma marubucin littafin, Dr. Charles Omole, ya bayyana cewa littafin ya tattaro tarihin rayuwar Buhari tun daga haihuwar sa har zuwa rasuwar sa.


