Zamu yi duk mai yiwuwa wajen samar da kayan aiki ga jami’an tsaro–Tinubu

0
8

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada ƙudurin gwamnatin sa na inganta tsaro ta hanyar samarwa da jami’an tsaro dukkan kayan aikin soja da na hukumomin tsaro domin murƙushe barazanar tsaro a faɗin ƙasar nan.

Shugaban ya bayyana hakan ne a jihar Legas yayin buɗe taron shekara-shekara na Babban Hafsan Sojojin Ƙasa na shekarar 2025. Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ne ya wakilce shi a wajen taron.

Tinubu ya ce gwamnatin sa ta riga ta fara sayo sabbin motocin yaƙi masu kariya daga nakiyoyi, sabbin motocin sulke, tare da gyara sama da motoci 100 na yaƙi domin ƙara kare dakarun soji.

Ya jaddada cewa tsaro muhimmin ginshiƙi ne a cikin manufar gwamnatin sa, yana mai cewa babu wata ƙasa da za ta bunƙasa ba tare da tsaro ba.

A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya yaba wa Sojojin Najeriya bisa ƙarfafa dangantaka tsakanin fararen hula da sojoji, tare da tabbatar da goyon bayan gwamnatin jihar ga rundunar soji.

Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya ce gwamnatin Tinubu za ta ci gaba da bayar da ingantaccen jagoranci da tsare-tsare domin ƙarfafa Sojojin Najeriya wajen fuskantar ƙalubalen tsaro.

Shi ma Babban Hafsan Sojojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya bayyana ƙaddamar da sabbin tsare-tsaren jin daɗin sojoji domin ƙara musu ƙwarin gwiwa da inganta ayyukan su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here