Wata majiya ta kusa da iyalan sa ta tabbatar da cewa marigayin ya rasu ne da safiyar Talata, 16 ga Disamba, 2025, a wani asibiti da ke Ƙasar Saudiyya, bayan fama da rashin lafiya.
Kungiyar Daliban Shari’ar Musulunci ta Najeriya (NAMLAS), ita ma ta tabbatar da rasuwar tasa a cikin wata sanarwar ta’aziyya da ta fitar a ranar Talata. A cikin sanarwar, kungiyar ta bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga ƙasa da bangaren shari’a.
Kungiyar ta miƙa ta’aziyya ga iyalan marigayin, bangaren shari’ar Najeriya, da al’ummar ƙasa baki ɗaya, tana roƙon Allah Ya gafarta masa, Ya kuma bawa iyalan sa haƙurin jure wannan rashi.
Ibrahim Tanko Muhammad ya rike muƙamin babban mai shari’a na ƙasa kafin ya yi ritaya, inda ya taka rawar gani wajen jagorantar bangaren shari’a a Najeriya.


