Tsananin sanyi ya yi ajalin ƴan ci rani a Maroko

0
12

Rahotanni daga arewacin Afirka sun nuna cewa wasu ’yan ci-rani tara (9) sun rasa rayukan su sakamakon tsananin sanyi a yankin iyakar Morocco da Algeria. 

Lamarin ya faru ne yayin da mutanen ke ƙoƙarin tsallaka iyakar domin ci gaba da tafiya zuwa Turai ta barauniyar hanya.

Kungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam a Maroko sun bayyana cewa gawarwakin da aka gani sun haɗa da maza bakwai da mata biyu, inda suka zargi jami’an tsaro da hana Mutanen  wucewa ba tare da tanadin kulawa ko agaji ba, abin da suka ce ya janyo mutuwar su a cikin sanyi mai tsanani. 

Sai dai har yanzu ma’aikatar harkokin cikin gida ta Maroko ba ta fitar da wata sanarwa kai tsaye kan lamarin ba.

Masana sun ce a ’yan shekarun nan, dubban ’yan ci-rani daga sassa daban-daban na Afirka na shigar da kan su cikin haɗarin tafiya Turai ta arewacin Afirka domin samun damar yin rayuwa a can. 

A kan hanya, da dama na fuskantar kifewar jiragen ruwa, tsananin sanyi, da kuma wahalar yunwa da ƙishirwa, lamarin da ke jawo asarar rayuka masu yawan gaske.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here