Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta nemi al’umma da su riƙa kai mata rahotanni in an fahimci faruwar wani abu da ya saɓawa ka’ida ko take dokokin shari’ar Muslunci.
Mataimakin babban kwamandan rundunar Dr. Mujahideen Aminuddeen, ne ya nemi hakan a yau Talata, yayin da yake jawabi dangane da yadda jami’an rundunar suka kama wata motar giya da aka shigo da ita daga Lagos zuwa Kano, bayan samun bayanan sirri.
Mujahideen, yace tawagar kwamandan sintiri ta Fagge ce ta samu nasarar kama giyar, wadda aka tabbatar da cewa wata mata ce ke turo ta daga Lagos zuwa Kano, kuma an samu samfurin giya kusan 13, ƙunshin kayan da aka kama.
Yace zuwa yanzu an kama matuƙin motar da ta ɗauko giyar don faɗaɗa bincike, tare da shan alwashin kama matar dake aiko da giyar zuwa Kano.


